An kebe matsayin shugaban kasa da ya kasance na jeka-na-yika, ga kabilar Kurdawa tunda aka fara gudanar da zabe mai jam’iyu da yawa a shekara ta dubu biyu da biyar, shekaru biyu bayanda Amurka ta jagoranci hambare gwamnatin shugaba Saddam Hussein.
Abdul-Mahdi wanda ya taba rike mukaman mataimakin shigana kasa, da ministan albarkatun mai da kuma ministan kudi, yana da kwanaki talatin ya kafa gwamnati ya kuma gabatar da sunayen ‘yan majalisa domin a amince da su.
Iraq dai ta gudanar da zaben majalisarta karon farko a watan Mayu, tunda aka murkushe kungiyar IS. Sai dai ba a sanar da sakamakon zaben ba, sai watan da ya gabata sabili da rigingimmun da suka barke dangane da sake kirga kuri’u.
Bayan an sake kirga kuri’un an tabbatar da cewa, jam’iyar babban malamin ‘yan shi’a Muqtada al-Sadr ce ta sami kuri’u mafiya yawa, ya kuma lashe kujeru hamsin da hudu cikin kujerun majalisa dari uku da ishirin da tara. Sai hadakar kungiyar da ta hada kan kungiyoyin mayakan ‘yan Shia tazo ta biyu da kujeru arba’in da bakwai, sai kuma hadakar kungiyar PM Haider al-Abadi tana biye da kujeru arba’in da biyu.
Facebook Forum