Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lumana Tana Iya Sauya Tarihi Inji Antonio Gutterres


Mahatma Gandhi-Tsohon Shugaban India
Mahatma Gandhi-Tsohon Shugaban India

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Gutterres ya yi kira ga kasashen duniya da su rungumi tsinkaya da hikimar Mahatma Gandhi tsohon dan fafutukar neman 'yancin kasar India.

Babban sakataren, ya yi wannan kira ne a yau da ake bukin ranar Lumana a duniya, wanda ake yi a ranar biyu ga watan Oktoban ta kowace shekara kuma ranar kenan da aka haifi wannan shugaba da ya samarwa India 'yancin kai, kana ya karfafa rajin kare hakkin bil Adama a duniya.

A cikin sakonsa na wannan rana, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, “ya ce yayin da duniya ta fada cikin rudanin tashe tashen hankula da kalubaloli da dama, akwai bukatar amfani da salon Gandhi na bin hanyar lumana wurin neman mafita. Yace a nan MDD, kawar da tashin hankali a duniya da kuma warware matsaloli ta hanyar lumana, suna cikin muhimman ayyukan mu”

Mr. Gutterres ya yi tunsarwa a kan kokarin Gandhi wurin tabbatar da adalci ga jama’a, a lokacin da ake samun rashin adalcin da dama. Ya ce akwai muhimmancin aiwatar da shirin adali a duniya tare da mutunta kowane dan Adam a wannan lokaci domin cimma dorewar muradun karni.

A cewar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, yarjejeniyar da ta kafa Majalisar da kuma kira da ta yi, a kan sasantawa, da shiga tsakani, da yin sulhu, da hukuncin shari’a da duk hanyoyin lumana na shawo kan barazana ga zaman lafiya a duniya, suna jaddada kalaman Ghandi cewa hanyoyin lumana wani karfi ne dake hannun mutane.

Ya ce Ghandi ya tabbatarwa duniya hanyoyin lumana za su iya sauya tarihi. Mr. Gutterres ya kammala jawabinsa ne da yin kira ga kasashen duniya su dauki darasi daga kwarin gwuiwa da salon Ghandi, "yayin da muke ci gaba da ayyukan zaman lafiya, da tabbatar da ci gaba da kare hakkin bil Adama ga kowane mutum a duniya".

A yau Talata biyu ga watan Oktoba kuma ranar cika shekaru 150 na haifuwar Mahatma Gandhi ce. Mr. Gutterres zai ajiye hure a dandalin Raj Ghat Memorial a birnin New Delhi, domin karrama Gandhi, a matsayin wani bangare na ziyarar aiki da yake yi a India a wannan mako.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG