Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Zargi China Da Kai Matsanancin Hasken Wuta Kusa Da Sansanin Sojinta Dake Afirka


Janar James Mattis, skataren tsaron Amurka
Janar James Mattis, skataren tsaron Amurka

Amurka ta dorawa China laifin kaiwa sansanin sojojinta dake Afirka matsanancin hasken wutan da ka iya yiwa dan Adam illa

Amurka tayi alkawarin cewa ba zata ga laifin kowa ba illa China, akan abinda ta baiyana barazana da kuma gangancin anfani da matsanancin hasken wutan nan daka iya wa dan adam illa a kusa da sansanin sojan Amurka dake Africa.

Kamar yadda jamiaan ma’aikatan tsaron Amurka, ke cewa,sunce wannan naurar an cillo ta ne daga sansanin sojan China dake Dorelah a kalla har sau ukku a lokutta badan-daban, wanda hakan ko ya haifar da rauni ga idanun wasu matuka jirgin saman Amurka.

Mai Magana da yawun maaikatan tsaron Amurka Dana White ta shaidawa manema labarai jiya alhamis cewa wannan ba karamar Magana bace.

Sai dai China bata mayar da martini ba nan take akan wannan zargin, amma tayi korafi a wani lokaci can baya cewa jiragen saman kasashen waje na mata liken asiri a sansanin ta na Djibouti, inji wata majiya dake da masaniya game da wannan lamarin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG