Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Dole A Gina Katanga Tsakanin Amurka Da Mekziko (Mexico)


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Yayin da ya ke jawabi gaban dinbin magoya bayansa, Shugaban Amurka Donald Trump ya kara jaddada cewa dole a gina katanga tsakanin Amurka da Mexico saboda tsaro.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar tsai da harkokin gwamnati zuwa karshen wannan shekarar muddun Majalisar Dokokin Amurka ta ki samar da isasshen kudin tabbatar da tsaro a kan iyakar Amurka, ciki har da kudin gina katanga tsakanin Amurka da Mexico.

A watan jiya Trump ya rattaba hannu kan wani kasafin kudi na dala tiriliyan 1.3 don gudanar da harkokin gwamnati zuwa karshen watan Satumba.

Da ya ke magana a wani wurin gangami jiya Asabar a garin Washington da ke jahar Michigan, Shugaba Trump ya ce Majalisar Dokokin za ta sake gabatar masa da kasafin kudi ranar 28 ga watan Satumba, kuma muddun kasafin bai kunshi kudin gina katanga ba, ba zai rattaba hannu a kai ba.

"Mu na bukatar katangar. Kuma lallai za mu samu cikakkiyar katanga," abin da ya gaya ma cincirindon jama'a kenan. Ya kara da cewa, "Kai hasali ma, an fara gida katangar. Mun samu dala biliyan 1.6. Za mu sake gamuwa ranar 28 ga watan Satumba kuma muddun ba mu samu kudin tabbatar da tsaron kan iyaka ba, to ba mu da wani zabi. Za mu rufe harkokin kasar saboda mu na bukatar tsaron a kan iyakokinmu."

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG