Bayan fitowar wani faifan bidiyo da ya bayyana yadda kungiyar 'yan ta'adda ta yiwa ma’aikatan agaji kissan gilla, Amurka ta bayyana takaicinta bisa yadda ‘yan ta'adda suka kashe ma'aikatan agaji su 5 a jihar Borno da ke shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.
Sanarwar da ta fito daga offishin jakadancin Amurka a Abuja, ta ce, ma’aikatan agajin sun sadaukar da rayuwarsu don tallafawa rayuwar wasu. Sannan Amurka ta mika sakon ta’aziya ga iyalai da ‘yan uwan ma’aikatan agajin.
Hajja Umma Bulama, mahaifiyar Abdulrahman Bulama daya daga cikin ma'aikatan agaji da ‘yan ta’addan suka kashe, ta shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, tana addu’ar Allah ya jikan su, sannan haka Allah ya kaddara, kuma sun bar komai ga Allah. Haka za lika tace tana godewa duk wanda yazo musu ta’aziyyar bisa ga wannan rashi da su ka yi.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, a ta bakin mataimakin sa Umar Usman Kadafur, ya ce, wannan abin bakin ciki ne, kuma gwamnati ba zata yi kasa a gwaiwa ba, zata ci gaba da yaki da ta’addanci.
Saurari rahoton Haruna Dauda Bi'u
Facebook Forum