Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta fitar sun nuna cewa an sami karin daruruwan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter wanda take sabunta alkaluman a kullum.
A cewar hukumar, mutum 543 ne cutar ta harba a jiya Laraba, wanda hakan ya mayar da adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar zuwa 38,344.
Hukumar ta kuma bayyana cewa mutum 15,815 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 813 suka mutu.
An sami sabbin alkaluman ne daga jihohi 24 kuma har yanzu jihar Lagos ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus, yanzu kuma ta sake samun mutum 180. Sai Birnin Tarayyar Abuja da ke bin ta da mutum 86.
Sauran jihohin da aka sami karin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Kaduna-56, Edo-47, Ondo-37, Kwara-35, Ogun-19, Rivers-19 ,Kano-17, Ebonyi-16, Enugu-16, Delta-7, Bayelsa-4, Bauchi-3, Abia-1.
Facebook Forum