Jiya Alhamis Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya kira Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, inda Pompeo ya jaddada muhimmancin dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin Mutane Najeriya da na Amurka, wanda hakan ke nuni da dacewar zuwan Shugaba Buhari Amurka kwanan nan.
Pompeo ya yi nuni da tasirin Najeriya a fadin nahiyar Afirka musamman kan batutuwa masu muhimmanci ga Amurka da Najeriya. Ciki da yaki da ta’addanci da kuma sauran abubuwan da ke barazana ga zaman lafiya da matakan tsaro, da kuma samar da sukunin bunkasa tattalin arziki, da yaki da almundahana, da kuma yada akidar dimokaradiyya da kwanciyar hankali.
Sakatare Pompeo ya yi fatan za a cigaba da hadin kai tsakanin kasashen biyu ta yadda kowacce za ta amfana.
Facebook Forum