Shugaban Amurka Donald Trump ya sa hannu a wata dokar kakabawa Rasha wadansu sababbin takunkumi, dokar da ta ba majalisar dokokin Amurka ikon hana shugaban kasar dagewa ko kuma soke takunkumin. Trump ya bayyana sabuwar dokar a matsayin mai cike da kurakurai, a wata sanarwar manema labarai da aka fitar jiya Laraba bayan ya sanya mata hannu. Duk da haka ya musanta cewa, an matsa masa ne ya sa hannu a dokar.
Sabuwar dokar da ‘yan jam’iyar Republican da na Democrat suka goyi baya, ta kakabawa Iran da Koriya ta Arewa da kuma Rasha takunkumi. Sanata Chris Coons, dan jam'iyyar Democrat daga Jihar Delaware, yayi marhabin da sanya hannu kan dokar.
Yace, "Naji dadi da shugaba Trump ya sa hannu a dokar kakabawa Rasha takunkumi. Ban yi tsammani yana da wani zabi ba, kasancewa majalisar dattawa da ta wakilai duka sun amince da dokar da gagarumin rinjaye".
Mai magana da yawun fadar White House, Sarah Huckabee Sanders, tace shugaba Trump ya sa hannu a dokar ne bisa dalilan hadin kan kasa.
Tace "Mun bayyana a fili cewa, zamu goyi bayan tsauraran takunkumi a kan dukkan kasashen uku, kuma zamu ci gaba da yin haka, babu abinda ya sake. Ina jin hakan ya bayyana a bayanan na yau".
Sai dai Trump yace dokar ta kunshi wadansu sharudda da ba zasu taimaki amurkawa ba, da zasu iya inganta dangantakar Rasha da Koriya ta Arewa da kuma China a maimakon cimma gurin da ake nema.
Facebook Forum