Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Lashi Takobin Hana Iran Mallakar Nukiliya


Donald Trump
Donald Trump

Amurka ta ce, ba za ta taba barin Iran ta mallaki makaman nukiliya ba, bayan da Iran ta sanar da cewa ta haura adadin da aka kayyade mata na tara sinadarin Uranium, kamar yadda ta amince a yarjejeniyar kasa da kasa ta 2015, mai tsai da shirin nukiliyar Iran.

A jiya Litinin ne fadar White House ta fada a wata rubutacciyar takarda cewa, ba za'a ba kasar Iran damar ci gaba da inganta sinadarin Uranium nata ba, kuma Amurka zata ci gaba da matsa mata lamba.

Za mu ci gaba da matsa wa kasar Iran har sai shugabannin kasar sun canza salo, a cewar fadar White House.

Da safiyar jiya Litinin ne Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na ISNA, cewa “Iran ta zarce adadin na kilo 300 Inda yanzu ya karu da kashi 3.67 cikin dari.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG