Wata gobara da sanyin safiyar yau ta lalata dubban na’urorin kada kuri’a da wasu kayayyakin zabe a birnin Kinshasa, kayayyakin da ya kamata a yi amfani da su a zaben shugaban kasar dake tafe a kasar Congo.
Barnabe Kikaya, mai ba shugaba Joseph Kabila mai barin gado shawara, ya ce an yi hasarar kusan na’urorin kada kuri’a 7,000 a gobarar da ta faru yau Alhamis da safe, wanda yace aikin bata-gari ne. Amma Kikaya yace, gobarar ba zata kawo wani cikas ga shirin zaben da ake yi na ranar 23 ga watan nan na Disamba ba.
An sha jefa alamar tambaya akan ko za a yi amfani da na’urorin kada kuri’ar yadda ya kamata a Congo ko a’a, kasar da rashin kayayyakin aiki suka dabaibaye, ga shi kuma ana nuna damuwa akan ta yiwu ayi magudi a zaben,, don dan takarar da Joseph Kabila ya tsaida, tsohon ministan cikin gidan kasar Emmanuel Ramazani Shadary ya sami nasara.
Ta yiwu zaben na ranar 23 ga watan Disamba, ya zama karon farko da za amika mulki ga wata gwamnati cikin lumana a tarihin kasar, tun bayan da ta sami ‘yancin kanta daga kasar Belgium a shekarar 1960.
Facebook Forum