Ma'aikatan ma’aikatar kudi ta kasa a jamhuriyar Nijar sun yi watsi da wani sabon tsarin gwamnatin kasar da ta fito da shi, a kasafin kudaden shekarar 2019, wanda ke takaita kudaden alawu da suka saba karba a matsayin alhakin ido, a duk lokacin da suka yi nasarar shigarda kudade asusun gwamnati.
Daruruwan ma’aikatan kudi ne suka amsa kiran hadin gwiwar kungiyoyin Fisamef a yayin gangamin da suka yi a ofishin ministan kudi, da zummar nunawa gwamnatin Nijar rashin amincewa da sabon tsarin biyan kudaden alawus-alawus, na ma’aikatan dake da alhakin tattaro kudaden diyyar kasa. SG na kungiyar jami’an kula da karbar haraji Snai Moussa Oumarou ya yi min karin bayani.
Dukkan wani yunkurin ganar da mahukunta rashin cancantar daukan wannan mataki ya citura, dalili kenan da kungiyoyi 5 na Fisamef suka fara tayarda magoya bayansu daga barci, inji Zakari Maman Moutari sakataren kungiyar ma’aikatan kudi ta Synatef.
Tuni dai majalisar dokokin kasa ta amince da tsarin kasafin kudaden 2019, ba tare da aiwatar da wani gyaran fuska ba akan abinda bangaren zartarwa ya gabatar, sai dai duk da haka wadanan kungiyoyin kwadugo sun lashi takobin tankwaso gwamantin ta canza ra’ayi akan kudirinta.
Kawo yanzu gwamnatin ta Nijar ba ta bayyana matsayinta ba, a hukunce akan wannan sabuwar dambarwa dake shirin tasowa a tsakaninta da wadanan jami’an, amma ministan kudi Massoudu Hassoumi dake kare manufofin gwamnati, a yayin mahawarar da majalisar dokoki ta gudanar a karshen mako, ya kira kasafin kudin na badi a matsayin mafi dacewa da bukatun kasa.
Facebook Forum