Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kammala Kwashe Dakarunta A Nijar


Wasu dakarun Amurka
Wasu dakarun Amurka

Wasu ‘yan tsirarun jami’an sojin da aka dorawa alhakin tsare ofishin jakadancin Amurka ne kawai suka rage, a cewar mai magana da yawun Pentagon Sabrina Singh.

Amurka ta kammala janye dakarunta daga Jamhuriyar Nijar kamar yadda wani jami’in Amurkar ya fada a ranar Litinin.

Wasu ‘yan tsirarun jami’an sojin da aka dorawa alhakin tsare ofishin jakadancin Amurka ne kawai suka rage, a cewar mai magana da yawun Pentagon Sabrina Singh.

A farkon shekarar nan ne sojojin mulkin Nijar suka ki sabunta yarjejeniyyar da ta baiwa dakarun Amurka damar gudanar da ayyuka su a kasar (dake yankin) yammacin Afirkar. ‘yan watanni bayan nan kuma jami’ai daga kasashen biyu suka fada cikin wata sanarwar da suka fitar na hadin gwiwa cewa dakarun Amurka zasu kammala kwashe sojojin su zuwa tsakiyar watan Satumba.

A watan jiya ne Amurka ta mikawa hukumomin Nijar sasanin sojin ta na karshe sai dai kuma, akalla sojojin dozen 2 sun ci gaba da zama Nijar, don gudanar da ayyukan da suka hada da tsara janyewar dakarun a cewar Singh.

Korar dakarun Amurka da Nijar ta yi bayan kifar da gwamnatin kasar a bara na da tasiri ga Washington domin ya tursasawa dakarun ta barin mahimman sansanonin da take amfani da su don gudanar da ayyukan yaki da ta’addanici a yankin sahel.#

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG