Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Makaman Nukiliya Data Kulla Da Rasha


Bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar Mallaka da Amfani da makaman nukiliya masu cin matsakai cin zango, shugaban Donald Trump, ya ce yana fatan nan gaba za’a kulla wata sabuwar yarjejeniyar da zata maye wannan da ta wargaje a yanzu.

A yau juma'a Amurka ta fice daga yarjejeniyar da ta kulla da Rasha kan mallaka da amfani da makaman nukiliya masu cin matsakaicin zango, domin ita ma ta kera nata sabbin makaman nukilyar, bayan da Rasha ta ki amincewa data lalata nata makaman na nukiliyar da kungiyar tsaro ta NATO ta ce mallakarsu ya karya yarjejeniyar da suka sakawa hannu.

“Rasha ta ki barin a gudanar da ingantaccen bincike wajen tabattar da gaskiya ko ta nakasa makaman nata, kamar yadda aka tanada a karkashin Yarjejeniyar”, a cewar Sakataren harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo. Ya kara da cewa Rasha ce ke da alhakin wargajewar wannan yarjejeniyar.

Pompeo, a cikin wata sanarwa, ya kara da cewa Amurka “ba zata zama ita kadai ce a cikin wannan yarjejeniyar da suka kulla ba wadda Rasha tana sane ta karya.

Sai dai kuma shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana fatan nan gaba za’a kulla wata sabuwar yarjejeniyar da zata maye wannan da ta wargaje a yanzu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG