Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Matukar Sha'awar Ganin Kasashen Turai Sun Kasance Daya


Barack Obama
Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya fara wani muhimmin zama na kwanaki biyu a Warsaw yau Jumma’a da Birtaniya inda zai bada karfi kan makomar kungiyar tsaro ta NATO bayan ficewar Birtaniya, daya daga cikin manyan abokan kawancenta daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Bayan ganawa da shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Birtaniya, Shugaba Obama ya bayyana yau Jumma’a cewa, Amurka tana matukar sha’awar ganin kasashen Turai sun kasance daya, kuma kowa yana son ganin an rage jan hankali, yayinda kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya suke kokarin kulla sabuwar dangantaka.

Shugaban Amurka yayi kokarin karawa shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai karfin guiwa, yayinda ake kara zaman zullumi a nahiyar game da hadin kan kungiyar bayan ficewa Birtaniya.

Da yake bayyana damuwar Amurka dangane da shawarar da Birtaniya ta yanke na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai, ganawar da shugaba Obama zai yi da shugaban majalisar Kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk da Jean-Cloude Juncker shine na farko tun isarshi Warsaw yau Jumma’a.

Karon farko a tarihin kungiyar tsaro ta NATO, tana da dakaru dubu goma sha uku yanzu haka da aka girke a kasar Spain, kasar da shugaba Obama zai yada zango bayan tashinsa daga Warsaw.

XS
SM
MD
LG