Janar Thomas Vandal, babban hafsan sojan dakarun Amurka a Koriya, da mataimakin harkokin tsaron Koriya ta Kudu Ryu Je-Seung ne suka yi wannan sanarwar ta hadin guiwa yau jumm’a a birnin Seoul.
Janar Vandal yace, “Koriya ta Arewa tana ci gaba da kera makaman nukiliya da makamai masu guba, sabanin yarjejeniyar kasa da kasa, da ta bukaci kasashen kawance su iya kare kansu idan suka fuskanci barazana.
Bayan gwajin makamai masu cin dogon zango da Koriya a arewa tayi a watan Fabrairu, Washington da Seoul suka fara tuntubar juna da tattauna yiwuwar girke na’urar kare makamai masu linzami da ake kira THAAD.
An kera na’urar ne da zata iya tarbewa ta kuma lalata makamai masu linzami a sararin sama, daidai lokacin da suke dab da isa zango. Kawo yanzu na’urar ta iya karewa da lalata makamai masu linzami gajere da matsakaicin zango.