Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Habasha Kawayen Kut-dat-kut ne-Shugaba Barack Obama


Shugaban Amurka Obama da na Habasha Melatu Teshume
Shugaban Amurka Obama da na Habasha Melatu Teshume

A cigaba da ziyarsa zuwa nahiyar Afirka shugaban Amurka Barack Obama ya isa kasar Habasha wadda ke ikirarin tana aiwatar da dimokradiya.

Shugaba Barack Obama ya ce Amurka da Habasha, kawaye ne na kut-da-kut da suka hada kai akan batutuwa da dama, sai dai ya nemi hukumomin kasar da su bar ‘yan jarida da bangaren ‘yan adawa su yi walwala ba tare da tsangwama ba.

A wani taron manema labarai da aka gudanar na hadin gwiwa a yau Litinin, tare da Firayim Ministan Habasha, Hailemariam Desaglegn, Shugaba Obama, ya yaba da irin habakar da Habasha ta samu ta fuskar tattalin arziki, inda ya kara da cewa an tsamo miliyoyin mutane daga kangin talauci, kana kasar tana taimakawa a yakin da ake yi da mayakan Al-shabab da ke Somalia.

Ya kuma kara da cewa a tattaunawarsu da Firayim Ministan, ya jaddada mai cewa tabbatar da walwalar ‘yan jarida da ‘yan adawa zai kara daidaita manufofin jam’iyya mai mulki a maimakon yayi mata zagon kasa.

Ana shi bangaren Firayim Ministan Hailemariam ya ce a shirye ya ke ya karfafa ‘yan cin dan Adam da shugabanci na gari, yana mai cewa karfafa mulkin dimokradiya da Habasha ke yi, ba abu ne na fatar baka ba kawai.

XS
SM
MD
LG