Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Wasu 'Yanbindiga Sun Kashe Mutane 14 a San Barnadino da Kuma Jikata 14


Wurin da aka kai hari a San Barnadino jihar California
Wurin da aka kai hari a San Barnadino jihar California

A Jiya Laraba mutane 14 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 14 suka samu rauni daban-daban sakamakon harbin kan mai uwa da wabi da wasu mutane ukku dauke da bindiga suka shiga wata cibiyar horas da nakasassu dake San Bernardino suka yi.

Sai bayan sun kwashe saoi ne yansanda suka yi nasarar kashe daya daga cikin su.Kana sauran suka tsere cikin wata mota amma daga baya 'yansandan sun ganosu har sun kashe biyu cikinsu kana suka kama daya.

Sai dai kafin wannan lokacin yan sanda sun dan jima suna kallon kalo tsakanin su da maharani a kusa da inda suka aikata wannan danyen aikin.

An nuno gawarwakin mutane a talabijin a kwakkwace dai dai inda maharan suka shiiga mota suka gudu, kuma an tsinci makami a kusa da wurin. San Bernadino dai nada tazarar tafiyar mil 60 zuwa Los Angeles. Babban jamiin yan sanda na wannan gari na San Bernadino Chief Jarrod Burguan ya shaidawa manema labarai cewa maharan sunzo cibiyar ne da niyyar yin kisa domin ko yace suna dauke da dogayen bindigogi ne.

Chief Burguan ya bayyana wannan harbin a matsayin wani taaddan ci na cikin gida, sai dai kuma yace kawo yanzu bai san dalilin wadannan maharan ba na aikata wannan aika-aikan.

Sai dai abinda bai fada ba shine ko wadanda suka mutun da wadanda suka ji rauni ma'aikata ne ko kuma masu hulda ne da wannan cibiyar.

Shima wani jami'in hukumar FBI yace masu bincike basu gano ko wannan harin yana da nasaba da ayyukan taaddanci na duniya ba ko kuma a’a.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG