Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed da tawagarta da sauran masu ruwa da tsaki, na ciki da wajen Najeriya, kamar su Mohammed Ibn Chambas, da wakili na musamman da gwamnan jihar Borno sun ziyarci garin Banki da ke karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
Tafiyar ta Amina ta ganewa idanunta irin halin da 'yan gudun hijira ke ciki, da yadda za a cigaba da tallafawa 'yan gudun hijirar, da har yanzu ke cigaba da samun matsugunai a wasu sannanonin.
A jawabinta, Hajiya Amina Mohammed ta ce sun je ne don su ga yadda ya kamata su taimaka ma mutanen da su ka samu dawowa, da zummar samar masu matsugunni wanda zai ma fi wuraren da su ka bari a baya. Wannan zai taimaka wajen ganin sun zauna lafiya, kuma cikin kwanciyar hankali.
Ta ce sun ziyarci wasu sansanonin ‘yan gudun hijirar, inda su ka kula cewa akasarin dubban mutanen da su ka tarar a sansanonin, su na sha’awar komawa gida, saboda su cigaba da gudanar da ayyukansu da rayuwarsu kamar yadda ya ke a baya.
Ta kara da cewar, abubuwan da su ka gani na daya daga cikin mafiya muni da su ka gani a yankin, amma ta ce akwai kuma wasu damarmaki da su ka gani.
Shi ma gwamnan jahar Borno Furfesa Baba Umara Zulum, ya ce koma ba komai zaman lafiya ya dada kankama a yankin. To amma ya ce jahar Borno na bukatar karin taimako don tinkarar wannan matsala, aikin maida mutanen garuruwansu na matukar bukatar kudi.
Ga Haruna Dauda Biu da cikakken rahoton:
Facebook Forum