‘Yan gudun hijiran da bala’in Boko Haram ya raba da gidaje, wadanda akasarinsu ‘yan jihar Borno ne, sun yi tattaki har zuwa Yola, hedikwatar jahar Adamawa daga sansaninsu dake garin Fufore domin bayyana halin da suke ciki, inda suka ce yau watanni hudu kenan rabon da a ba su abinci, lamarin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.
‘Yan gudun hijiran mazansu da matansu, sun bukaci Shugaba Buhari da kuma gwamnatin jihar Borno da su yi wa Allah da annabinsa su duba halin da suke ciki a yanzu.
Umar Bakura na daga cikin shugabanin ‘yan gudun hijirar da ke sansanonin da aka tanadar, kuma ya yi Karin haske game da Wannan hali da suke ciki.
Ita ma shugabar mata na ‘yan gudun hijira ta ce yanzu haka mata da kananan yara na cikin halin ni ‘yasu. Mr Midala Anuhu, jami'in riko na Hukumar Bada Agajin Gaggawa a Najeriya ta NEMA mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, wanda ita ke kula da sansanonin, ya ce laifin ba daga garesu ba ne, inda ya ce sun rubuta bukatar bada abincin ga ‘yan gudun hijirar zuwa ga shelkwatar hukumar da ke Abuja, to amma har yanzu basu sami amsa ba, inda ya bukaci ‘yan gudun hijiran da su kwantar da hankulansu.
Kamar yadda alkalumma suka nuna, baya ga wadanda suka rage a sansanonin da aka tanadar, yanzu haka akwai wasu ‘yan gudun hijiran da ke samun mafaka a gidajen ‘yan’uwa ko kuma majami'u wanda don haka tuni wata majami'a ta kaddamar da gidauniyar gina gidaje ga ‘yan gudun hijira domin basu mafaka.
Ga Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum