Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ilmantar Da 'Ya Mace Na Habaka Tattalin Arzikin Kasa


Ummul Khairi Alhassan
Ummul Khairi Alhassan

Ta fuskanci kalubale da dama a yayin da ta je yi ma kasa hidima karkashin shirin NYSC sakamakon al’adarsu ba iri daya da wadda ta saba ba, domin a kauyen da aka kai ta ba’a kashe maciji duk wanda ya kashe sai ya yanka shi, alhali kauyen a cike yake da macizai kamar yadda Ummul Khairi Alhassan ke bayyanawa Dandali.

Ta kara da cewa kauyen na da al’adar cewar duk wanda maciji ya sara lallai yana da mummunar akida, ko danginsa suna da wani dabi’a da ba ta da kyau, wanda wannan sabon abu ne a wajenta da kuma al’adarta.

Yayin neman kwas da za ta karanta a makaranta sakamakon rashin samun maki mai yawa a jarrabawar JAMB ya sa ta sami kwas din Cooperative Economics and Management Studies.

Ummul Khairi ta ce tana kammala yi wa kasa hidima ta samu aiki inda ta sha gwagwarmaya da maza a wajen aikinta inda mazan kan ce mata sun cika tsantseni, da bin ka’ida a wasu lokutan ma sukan yi mata wani kallo da tunanin mata ba za su iya aiki yadda ya kamata ba.

Amma ita kuwa ba ta bari wannan tunanin nasu ya shafi yadda take gudanar da aikinta ba.

Daga karshe tana mai bai wa mata shawarar cewar, ilimantar da diya mace tamkar ilmantar da alumma ne domin ko 'ya mace ta samu ilimi za ta ilmanatar da 'ya'yanta da ma na makwabtanta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG