A wani taron karawa juna ilimi da cibiyar bincike da inganta magunguna daga tsirai ta Afirka dake Jami’ar Jos ta shirya wa masu binciken magunguna, masanan sun gano cewa nauin wani kuda yana da yanayin da ya yi kama da na dan Adam da za’a iya yin anfani da shi a samu warkar da wasu cututtukan da suka shafi kwakwalwa, da cutar sankara, da cututuka masu yaduwa da ciwon sikari da dai makamantansu.
Dr. Abolaji Amos daga Jami’ar Ibadan ya ce kasashe da dama sun yi anfani da kudan wajen gudanar da binciken wasu cututuka kuma sun samu nasarar samar da magunguna har ma da lambobin yabo. Idan an yi anfani da kudan a Najeriya zai taimaka wajen yakar mafi yawan cututukan da ake fama dasu.
Idan an durawa kudan cutar sikari kuma za’a ga alamar yawan sikari a jikin kudan daga nan sai a nemi maganin da za’a sawa kudan ya warke.
Malam Hassan Abdullahi daga asibitin gwamnatin tarayya dake Keffi a jihar Nasarawa ya yiwa Muryar Amurka karin haske kan nauin kudar da amfaninsa. Y ace kudan baya yada cuta kuma tsirai yake ci irin su mangwaro ya tsotsa ya ci gaba da rayuwarshi. Injishi masana sun gano cewa duk abun da mutum ke iya yi kudan ma na iya yi. Ana kuma iya sawa kudan cutar da ake son a san maganinta.
Shi ma Jibrin Ibrahim dalibi dake neman digirin digirgir a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ya halarci taron. Yace duk da yana son yin bincike amma babu kudin yin hakan kuma idan an samu an yi binciken, babu wata hanyar yabawa wanda ya yi binciken kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.
Ga karin bayani daga rahoton Zainab Babaji
Facebook Forum