Allah ya yiwa Alhaji Yusuf Buratai, mahaifin Janara Yusuf Tukur Buratai, rasuwa a asibitin koyaswa na Jami'ar Maiduguri bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya .
An yi jana'izar mahaifin babban hafsan sojojin Najeriya din ne yau inda manyan jami'an gwamnatin tarayya da na jihohi suka kasance.
Alhaji Yusuf Buratai, wanda shi ma tsohon soja ne, ya rasu yana da shekaru 106 ya kuma haifi 'ya'ya fiye da 20. Guda 15 yanzu suna raye. Goma cikinsu mata ne. Guda biyar kuma maza ne cikinsu har da babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai.
Jana'izar ta samu halartar gwamnan Borno Kashim Shettima da kwamishanoninsa da 'yan majalisu da shugabannin riko na kananan hukumomi da kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas da sauran manyan jami'an soja dake aiki a jihar.
A bangaren gwamnatin tarayya mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro Janar Baba Gana Monguno mai ritaya ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayyan zuwa jana'izar. Tawagar ta hada da ministan tsaron kasa Mansur Dan Ali da Ministan ayyuka da gidaje, Alhaji Baba Shihori da Babban hafsan sojin sama, Sadique Abubakar da dai sauransu.
Haruna Dauda na da karin bayani a rahotonsa
Facebook Forum