Rundunar Sojan Najeriya Ta Amince Ta Gaza Kwato Daukacin ‘Yan Matan Chibok
Rundunar sojan Najeriya mai kula da yaki da kungiyar Boko Haram tace daga shekaru biyu da suka gabata lokacin kawo yanzu ta samu nasarar kwato mutane 30,000 daga hannun ‘yan kungiyar boko haram.
Da Yake maganada da Muryar Amurka, Ministan tsaron Najeriya,Janar Mansur Dan Ali mai ritaya yace sojoji sun taka rawar gani wajen murkushe kungiyar ta boko haram.
Ministan yace yanzu haka ba wani yanki dake karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram sabaninabinda ke faruwa da.
Shima da yake tsokaci game da wannan yakin da suke yi da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, shugaban rundunar sojojin dake wannan aiki, Manjo janar Rogers Ibe Nicholas, yace yanzu haka sunyi nasarar karbe babban hedikwatar ta kungiyar boko haram dake cikn dajin Sambisa.
Yace duk da yake basu samu nasarar kwato daukacin ‘yan matan chibok ba da kungiyar ta sace yau sama da shekaru 4,duk da haka dai tayi nasarar kwato farar hular da ‘yan kungiyar suka kame suka tilasta su zama cikin su.
Jami'an gwamnatin Najeriyan biyu, sun shaidawa wakilin gidan Radiyon nan na Muryar Amurka James Butty cewa, sojoji Najeriya ba zasu yi kasa a gwiwa ba har sai sun tabbatar ba sauran ya’yan wannan kungiyar.
Facebook Forum