Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwace Takardun Sanusi Lamido


Tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasar Sanusi Lamido.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasar Sanusi Lamido.

Hukumomin tsaro a najeriya sun kwacewa tsohon gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi takardun tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a daren Juma’ar nan, duk kuwa da umarnin babbar kotun tarayya dake Lagos na hana gwamnatin kasar daukar irin wannan mataki akansa.

Wannan lamarin ya faru na tashar jirgin sama na Mallam Aminu Kano, a lokacin da Sanusi Lamidon yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Paris dake kasar Faransa.

Wakilin Muryar Amurka, Mahmoud Ibrahim Kwari ya tattauna da Mr. Sanusi.

“Da zan je Faransa, to har kayanmu sun riga sun wuce, an bamu takardun shiga jirgin sama, wato ‘Boarding Pass’, mutanen SSS suka ce an rike Fassfo din daga ofishin Shugaban Kasa, suna da umarni, kada na fita,” a cewar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Mr. Sanusi ya cigaba da cewa “babu wanda ya bada wata hujja, babu wanda yayi wani bayani, kuma na nuna musu odar Kotu na cewa kada su shiga harkata, su bani ‘yanci na dan Adam, su barni nayi tafiya inda nake so inyi tafiya, amma sunce suna da umarni, kuma akan umarni suke aiki.”

Sanusi Lamido ya bayyana cewa zai koma kotu.
“Abune da muke gani, na kasarnan, na wato mulki na kama karya, da kuma rashin bin doka. Sannan lauyoyi na su koma wajen alkali su gaya mishi ga abunda gwamnati tayi.

Yaya masana shari’a suke kallon wannan lamari na kwace Fassfo? Barrista Fatihu Abba lauya ne a Kano.

“Wannan taka shari’a ne, yadda duk baka zata, an je kotu, dake da hurumi, tace Mr. Lamido zai iya zuwa duk inda yake so a duk fadin duniya. Alkali ya bayarda hukunci, don haka gwamnati bata da ikon hana shi fita, ko walwala a kasarnnan.” Inji Barrista Abba. “Wannan taka doka ne.”

A kwanakin baya, Sanusi Lamido kafin a dakatar dashi daga kan matsayinsa, ya fito yayi magana akan bacewar makudan kudade, wanda hakan ya jawo ce-ce kuce, daga baya aka bayyana sanarwar dakatar dashi.
XS
SM
MD
LG