Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka Ta Kudu Na Daga Cikin Kasashen Dake Hada Kai Da ‘Yan Sandan Kasar China - Rahoto


Yan Sandan Kasar China
Yan Sandan Kasar China

A kwanakin baya ne ministan 'yan sandan Afirka ta Kudu Bheki Cele da tawagar manyan jami'an 'yan sanda suka dawo daga ziyarar da suka kai kasar China, inda suka tattauna kan karfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda.

“Ma’aikatar tana da yakinin cewa za a iya magance matsalolin laifuffukan da ke faruwa a kasar, idan har muka kara kaimi wajen aikin ‘yan sanda. Wannan ne ya sa kasar ke binciko duk wata hanya ta wannan fanni ciki har da hadin gwiwa da jami'an tsaron kasar China don taimakawa wajen ci gaban fasaha,” in ji kakakin ma'aikatar 'yan sanda Lirandzu Themba ga Muryar Amurka.

Sanarwar da 'yan sandan suka fitar ta ce, ziyarar ta kwanaki biyar ta tawagar ta hada da ziyarar ofisoshin 'yan sanda a birnin Beijing da Shanghai da Shenzhen, da yin aiki a jami'ar tsaron jama'a ta kasar China, wata cibiyar horar da kwararru.

"Mambobin kungiyar dakarun SAPS ta musamman irin su National Intervention Unit (NIU) da Special Task Force (STF) kwanan nan sun sami horon yaki da ilimi kuma sun kammala horo na musamman," in ji sanarwar.

Minista Cele ya kuma gana da ministan tsaron jama'a na kasar China, Wang Xiaohong. Babbar ajandar itace "kafa tsarin musanyar 'yan sanda na yau da kullun na iya aiki da horarwa tsakanin kasashen biyu

Kasashen biyu sun kuma tattauna kan shirye-shiryen tsaro na taron kolin kungiyar BRICS mai zuwa. Ana gudanar da taron ne a birnin Johannesburg a watan Agusta kuma zai samu halartar shugaban kasar China Xi Jinping.

XS
SM
MD
LG