Mayakan Kungiyar al-Shabab sun kai wasu hare hare guda biyar bisa a sansanonin sojojin Somalia a yakin kasar da ake kira Lower Shabelle, kuma akalla mayakan sa kan guda 12 aka kashe, kamar yadda shaidu da jami'an gwamnati suka yi bayani.
Jami’an Somalia sun ce an tarwatsa wasu manyan motoci biyu da aka dankarawa bamabamai a jiya Lahadi a sansanin dakarun Afirka da ake kira AMISOM a takaice a garin Bula Marer, mai tazarar kilomita 110 daga kudancin babban birnin kasar Mogadishu, kuma babban gari a cikin yankin. Nan da nan mayakan kungiyar na kasa suka farwa sansanin.
Jim kadan bayan harin farko, sai wata karamar motar safa ta tinkaro wani sansanin AMISOM dake kusa da kauyen Golweyn kuma kuma nan ta tarwatse.
Al-Shabab ta kaiwa sansanin Sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirkan na uku a garin Barawe da kananan bama bamai. Yan bindigar sun kuma kai kai hare hare a kan sansanonin sojin Somalia bisa tsari a garuruwar Qoryoley da Mashallay.
Mataimakin gwamnan yankin Lower Shabelle Ali Nur Mohammed ya shaidawa sashen Somalia na Muryar Amurka cewa sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka da sojojin Somalia sun dakile duk hare haren.
Mazauna garin Bula Marer sun ce akwai wadanda suka mutu a cikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Afirkan da ake kira AMISOM, amma kuma basu da masaniya kan yawan su saboda jami'an sun killace sansanin.
Facebook Forum