Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Miliyan Hudu Na Fama Da Karancin Abinci A Arewacin Najeriya - MDD


Matsalar karancin abinci a Najeriya.
Matsalar karancin abinci a Najeriya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan hudu a arewa maso gabashin Najeriya na fuskantar matsanancin karancin abinci, yayin da tallafin da kasashen duniya ke bayarwa yake raguwa.

Sama da yara 700,000 a jihohin Borno da Adamawa da Yobe na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lamarin na iya yin muni a tsakanin watan Yuni zuwa Satumba, abin da ake kira 'tazarar yunwa' lokacin da hajojin abinci daga girbin da aka yi na baya ya kare.

Haka kuma an sami cikas ga noman da aka yi a shekarar da ta gabata, sakamakon ambaliyar ruwa mafi muni da Najeriya ta fuskanta cikin shekaru goma.

Kodineta na Majalisar Dinkin Duniya Matthias Schmale ya ce "Idan kadada 600,000 na gonakin noma suka lalace, ko kuma aka lalatar da su, nan gaba za a fuskanci matsanancin karancin abinci."

Karancin abincin dai ya samo asali ne sakamakon yakin da Rasha ke yi a kasar Ukraine da rikicin baya-bayan nan a Sudan.

Sai dai jami'ai sun ce hauhawan farashin kayayyaki a Najeriya da kuma manufar sake fasalin kudi na baya-bayan nan sun kawowa mutane matsalar damar sayen abinci.

Manajan kula da abinci mai gina jiki na UNICEF, Karanveer Singh, ya ce duk da muhimmancin agajin da ake karkata zuwa ga wasu matsalolin gaggawa na duniya, har yanzu Najeriya na samun kayan abinci.

Jami’an tsaron Najeriya sun yi matukar dakile karfin fadan ‘yan bindiga da ake fama da su.

Amma har yanzu kasar na cikin yaki. Kuma har sai an kare, sannan miliyoyin mutane za su yi yaki da wani nau'in yake-yake – wato yunwa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG