Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Abun Dubawa Tsakanin Majalisar Dattawa Da Bangaren Shugaba Buhari


Ba tun yanzu ake kai ruwa rana tsakanin bangaren majalisar Najeriya da kuma shugaba Buhari ba, batun da masana ke ganin akwai abin dubawa, musamman ganin yadda wasu kungiyoyi a kasar ke barazanar mamaye zauren majalisa bisa abin da suke ganin bijirewa shugaba Buhari da suke zargin ‘yan majalisar kasar ke yi.

Koda shike jam’iyar APC dake mulkin kasar ta kafa wani kwamitin shiga Tsakani sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan majalisar dattawa dana wakilai suka soma gamuwa da fushin ‘yan gani–kashe nin Buhari.

To wai ko me masana ke cewa game da wannan danbarwar siyasar?

Hon. Abdullahi Prembe, tsohon kwamishinan yada labaran jihar Adamawa, kuma masanin siyasa yace, wannan shine gishirin siyasa kuma dan haka akai zuciya nesa.

Shi kuwa wani masanin Dr Amuga Keftin Na-Mala, malami a jami’ar Modibbo Adama, dake Yola, yace ai maimakon mamaye majalisa kamata yayi jama’a su bi yadda doka ta tsara, akan ko wane dan majalisa.

Mallam Oska, wani dan gani kashenin jam’iyyar APC ne, na ganin akwai bukatar tsoma bakin manyan kasa don shiga tsakani tunda ko wane bangare na cin gashin kansa.

Ibrahim Abdul’Aziz ya hada mana wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG