Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Hadakar 'Yan Adawa A Nijar Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda


Wasu 'yan adawar Nijar
Wasu 'yan adawar Nijar

Gamayyar kawancen jam'iyyun adawa da ake kira FUWA a jamhuriyar Nijar ne suka shiga zaman dirshan tun ranar Lahadi a dandalin taron jama'a a birnin Yamai domin jaddada kin amincewarsu da kasafin kudin 2018 na kasar da suka ce ya cuci talakawa, lamarin da ya sa 'yan sanda suka cafke wasu shugabanninsu

Shugaban jam'iyyar PNPD Alhassan Mamba na kawancen adawa mai zaman kansa wato FUWA, da Ibrahim Bala na jam'iyyar MODEN Lumana mai adawa da gwamnatin Issoufou Mahammadou na cikin mutane goman da suka shiga hannun 'yan sanda yayinda suke zaman dirshen a birnin Yamai.

Manufar zaman dirshen din ita ce jaddadawa mahukuntar kasar da rashin amincewarsu akan wasu batutuwan da suka hada da tsarin kasafin kudaden 2018 wanda suke yiwa kallon haramtace saboda a cewarsu ya kunshi dimbin haraji dake jefa talakawa cikin tsadar rayuwa.

Sakataren jam'iyyar PNPD Sise Yau Useini ya gayawa manema labarai cewa yayinda suke zaman dirshen 'yan sanda suka shiga harabar suka kama mutane goma daga cikinsu cikin dare. Da safiya tayi injishi, sun tafi ofishin 'yan sandan amma ba'a bari sun gansu ba baicin mutum guda.

Sai dai a Nijar yin kwaranniyar tsakar dare ba tare da izinin hukuma ba laifi ne shi ne kuma ake zargin 'yan siyasan da aikatawa wadanda yanzu suna tsare a ofishn 'yan sandan farin kaya.

Sai dai kakakin gwamnatin Nijar ministan raya al'adu Asmana Malam Isa ya ce babu hannun gwamnati cikin al'amarin. A cewarsa magana ce da tuni ta kama hanyar zuwa kotu saboda haka gwamnati bata da ta cewa domin kaucewa yin shishshigi ga harkokin shari'a.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG