Hajiya Aisha Buhari ta yi wannan kira ne a jihar Bauchi wajen bikin yaye rukunin mata da matasa har dubu ‘daya, da aka koyawa sana’o’i iri daban-daban domin su sami abin dogaro da kai.
A nata jawabin mai dakin gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Mohammad Abudullahi Abubakar, tace jihar Bauchi na alfahari da irin gudunmawar da suke samu daga shirin tallafin da Aisha Buhari ke baiwa jihohin kasar.
Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, yayiwa Hajiya Aisha godiya saboda kirkiro gagarumin shirin baiwa mata hanyoyin koyon sana’a don gogaro da kai.
Wakiliyar mata da matasa da suka amfana daga wannan shiri, Rabi Usman, tace a madadin duk mata da matasan da suka koyi sana’o’i karkashin shirin suna mika sakon godiyarsu.
Sai dai kuma shugaban kungiyar kare muradun nakasassu a Najeriya, Hamza Waziri Mohammad, yace su ma suna bukatar tallafin da zai sa su zamo masu dogaro da kai, a maimakon basu kekunan guragu dake sasu yawon bara.
Domin karin bayani ga rahotan Abdulwahab Mohammad.
Facebook Forum