WASHINGTON, DC —
Babbar jami’ar hukumar kula da kare hakkokin Bil Adama a kasa da kasa, tace rikicin kabilanci da ake yi a jumhuriyar Afirka ta tsakiya naci gaba da kazancewa saifa an tashi tsaye sosai kafin samun nasarar maido da zaman lafiya.
Babbar jakadiyar MDD mai lura da ayyukan kare hakkin Bil Adama Navi Pilly a jawabin da ta yiwa taron manema labarai yau Alhamis a birnin Bangui tayi kiran da a karfafa daukan wasu matakan domin a sami kaiwa ga warware matsalolin dake janyo rashin zaman lafiya a yankin.
Jakadiyar tana mai cewa matsalar karkashi mutanen da ake yi yanzu a yankin na ci gaba da kazancewa. Bayan kisan kai, ana ci gaba da muzgunawa farar hula, wasu ana konesu su mutu har lahira. Shaidun gani da ido sun tabbatar da wannan aika-aikr a wurare hudu.