Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Zasu Ba Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Agajin dala Miliyan 314


'Yan Najeriya da aka kwaso daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a saboda tashin hankali
'Yan Najeriya da aka kwaso daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a saboda tashin hankali

Kungiyar Tarayyar Afirka ce ta bayyana wannan yau asabar a karshen taron masu bayar da agaji a kasar Ethiopia.

Kasashen waje masu bayar da agaji sun yi alkawarin bayar da karin dala miliyan 314 domin taimakawa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda ta tsunduma cikin yanayi na fitina da rashin tsaro tun lokacin da 'yan tawaye suka hambarar da shugaban kasar a shekarar da ta shige.

Yau asabar Kungiyar Tarayyar Afirka ta ba da sanarwar sabon agajin kudin a karshen taron neman agajin da aka gudanar a kasar Ethiopia.

A wajen wannan taro na yini guda, wakilai daga fadin Afirka da kuma na wasu kasashen duniya sun yi alkawarin bayar da tallafin kudi ga rundunar kiyaye zaman lafiyar da kasashen Afirka suke jagorancinta a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

An girka dubban sojojin wannan runduna da ake kira MISCA a takaice da kuma na kasar Faransa a kasar domin kawo karshen mummunan zub da jinin addinin da ya yi tsanani a kasar.

A yau asabar din, wani kwamandan sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka dake jamhuriyar, yace rundunar MISCA ta karbe ikon wani garin dake kusa da Bangui, babban birnin kasar, inda a farkon mako 'yan tawaye dauke da manyan makamai suka fara hallara.

Taruwar tsoffin mayakan kungiyar Seleka a garin Sibut ta tsoratar da mazauna wannan garin.
XS
SM
MD
LG