Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka ta Tsakiya: Da Gagarumar Rinjaye 'Yan Kasar Suka Amince da Sabon Kundun Tsarin Mulkin Kasa


Sojojin Majalisar Dinkin Duniya dake kiyaye zaman lafiya a Afirka Ta Tsakiya
Sojojin Majalisar Dinkin Duniya dake kiyaye zaman lafiya a Afirka Ta Tsakiya

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bisa dukkan alamu masu zaben kasar sun amince da gagarumar rinjaye sabon tsarin mulkin kasa da aka yi da niyyar kawo karshen tarzoma da zubda jini a kasar da ake tayi fiye da shekaru uku, tsakanin musulmi da kirista.

A kwarya-kwaryar sakamakon zaben raba gardamar da aka yi ranar lahadi ya nuna kashi 90 cikin dari na masu zabe sun amince da tsarin mulkin. An dakatar da zabe a wasu sassan kasar inda mayakan sakai suka yi barazanar tada tarzoma, ciki harda unguwar da musulmi suke a birnin Bangui. Har yanzu ba'a kidaya kuri'n ba.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe mutane biyar, akalla wasu 20 kuma sun jikkata a ranar Lahadin, lokacinda masu goyon bayan kudurin da masu adawa suka yi musayar harbe harbe da bindigogi a Bangui.

A ranar Laraba,daruruwan mutane ne suka yi maci zuwa helkawatar sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake fadar kasar, suna neman cewa "tilas ne a kori makiya zaman lafiya."

Idan har aka amince da shi, sabon tsarin mulkin, zai takaita wa'adin mulkin shugaban kasa, zuwa wa'adi biyu kadai, na shekaru biyar biyar, rage karfi ko ikon da sojojin kasar suke da shi, da kuma tabbatar da 'yancin yin addinin.

XS
SM
MD
LG