Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Francis Ya Fara Ziyarar Kwana Shida a Nahiyar Afirka


Paparoma Francis a kasar Kenya inda ya fara ziyarsa
Paparoma Francis a kasar Kenya inda ya fara ziyarsa

Jiya Laraba da rana Papa Roma Francis ya sauka a birnin Nairobin Kenya, inda ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Uhuru Kenyata, tareda tawagar makada da mawaka da masu raye raye. Wannan ne zangonsa na farko a ziyarar kwanaki shida da zaiyi a Afirka da zata kaishi Uganda da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

'Yan kasar Kenya sun fara hallara kan babbar titin da Fafa Roman zai bi 'yan sa'o'i kamin ya isa.

"Yan kasar mabiya darikar Katholika da ma wadanda basa bi duk suna cike da doki da murnar wannan ziyara.

Kokarin hada kan jama'a daga kabilu da addinai daban daban yana daga cikin manyan burin Papa Roma Francis kuma ya tabo hakan a jawabin da yayi a gidan shugaba Kenyatta.

Yace"tarihi ya nuna tarzoma, da ta'adanci da wasu rikice-rikice suna samun kafuwa ne daga tsoro, da rashin yarda, da kuma cire tsamani daga rayuwa sakamkon talauci da kunci," inji Papa Roman. Daga karshe yace hakkin mutane ne da suka hakikance kan manufofin kirkiro da kasa da su yaki irin wannan tunani.

Kenya ta fuskanci hare haren ta'addanci daga mayakan sakai na kungiyar al-Shabab, yayinda a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, zangon Papa Roma na karshe, har yanzu tana fama da fitinar kan sabanin akida.

Da aka tambayeshi baya fargaban tarzoma a yayin wannan ziyara, Papa Roma Francis ya kada baki yace, "yafi damuwa da sauro".

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG