Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Adamawa Sun Shirya Tsaf!


Masu kada kuri'a a Najeriya a rumfar zabe.
Masu kada kuri'a a Najeriya a rumfar zabe.

Yankin Admawa dai da Taraba na daya daga cikin yankunan da suke fama da matsalar ta’addanci a Najeriya, amma sun ce sun shiryawa zaben 28 ga watan Maris na Najeriya.

Zaben gobe yana ci gaba da samun shiryawar hukumomin jihohin Najeriya, kamar yadda a jihar Adamawa Alhaji Baba Abba Yusuf, kwamishinan zaben jihar Adamawa ya bayyana cewa kuri’ar da za a dangwala hannu akai ta zaben shugaban kasa kalarta Ja ne haka kuma akwatin jefata ma Ja ne.

bakar takardar kuri’ar Sanatoci da akawati jefawa kuma baki ne. Sai kuri’ar ‘yan majalisa da akwatin jefawa kuri’a su kuma koraye.

Kamar Adamawa, a jihar Taraba ma an gama shiryawa tsaf in ji kakakin hukumar zaben jihar Mista Fiben Yameh da yake Magana da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz. Adaji Gebrail ne kwamishinan ‘yan sandan jihar.

Ya tabbatarwa Muryar Amurka cewa sun gama shiryawa tsaf sannan ba zasu dauki wargi ba, haka kuma ya jaddada cewa in ka dauke gwamnan jihar ba wanda zasu yarda ya je wajen kada kuri’a da jami’an tsaro.

Yanzu dai lokaci ne kadai zai iya tabbatar da yadda zaben na gobe zai kaya. Haka kuma ana ci gaba da maida ‘yan gudun hijira yankunansu na Michika da Madagali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG