Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwmnatin JIhar Taraba Na Shirin Sayar Da Kaddorin JIhar


Gwamnan Jihar Taraba mai rikon kwarya.
Gwamnan Jihar Taraba mai rikon kwarya.

Kungiyoyin cigaban jihar Taraba,sun kushewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sayar da wadansu kadarorin gwamnatin jihar da suka da jiragen saman jihar, da wadansu gidajen gwamnatin jihar dake biranen Abuja, da Kaduna.

Yanzu haka dai jama’a da kuma wasu kungiyoyin cigaban jihar Taraba,sun fara maida martani game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sayar da wadansu kadarorin gwamnatin jihar da suka hada da wadansu jiragen saman jihar, da wasu gidajen gwamnatin jihar dake biranen Abuja,da Kaduna batun da 'yan jihar Taraban ke ganin bai dace ba.

Wadansu kungiyoyin cigaban jihar sun kira wani taron manema labarai domin nuna fushi da kuma kin amincewa da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka musamman a wannan lokaci da bai wuce watanni biyu ba a kafa sabuwar gwamnati.

Da yake maida martani dangane da lamarin, mukaddashin gwamnan jihar Mr. Sani Abubakar Danladi yace gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne domin samun kudaden shiga.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Ibrahim Abdul’Aziz ya aiko mana da Yola

Rahoton Sayar Da Kaddarorin Jihar Taraba
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG