Wannan kuma na zuwa ne yayin da al’ummomin yankin ke ci gaba da gudanar da bukukuwan samun zaman lafiya, biyo bayan kwato yankin daga hannun mayakan Boko Haram.
Kamar yadda rahotanni daga yankin na Madagali ke bayyanawa ‘yan bindiga masu tada kayar bayan na kokarin sake kai mummunan farmaki ne, to amma kuma basu taki sa’a ba, inda sojoji da kuma yan sakai na maharba suka yi musu kofar rago.
Wani dan sakai na maharba yace sun yi yunkurin kai harin ne a gefen Waga Chakawa dake kusa da dajin Sambisa, inda yace an kashe mayakan Boko Haram da dama.
Shima kwamandan yan sintiri na vigilante a jihar Adamawa, Adamu Abdullahi ya tabbatar da faruwan lamari da ma irin nasarar da aka samu akan yan kungiyar ta Boko Haram.
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umman ta Madagali ke bukukuwan murnar samun zaman lafiya. To ko yaya al’umman yankin suka ji da wannan yunkuri na Boko Haram. Yusuf Mohammad, dake zama shugaban karamar hukumar ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana hadin kan da ake samu a yanzu.
Madagali dai itace karamar hukumar farko da mayakan Boko Haram suka fara kwacewa a jihar Adamawa, inda suka ci karensu babu babbaka kafin daga bisani dakarun Najeriya suka kwato yankin, wanda kuma kawo yanzu akan dan samu harin sari –ka-noke a wasu lokutan, batun da dan majalisar wakilai mai wakiltar Madagali da Michika Mista Adamu Kamale, ya yi kira da a kara sansanonin soji a yankin.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum