WASHINGTON, DC —
Babban hafsan mulki na rundunar sojan kasa ta Najeriya, manjo janar I M Alkali da babban kwamandan shiyya ta 7 ta sojojin kasa, Birgediya janar Victor Ezugu, sun tsallake rijiya da baya a lokacin da suke kan hanyar zuwa Pulka.
'Yan kungiyar boko haram sun binne Bama bamai hudu a kusa da mararrabar Banki wanda naurorin sojojin suka gano aka kuma samu nasarar tonowa da tarwatsawa.
Hafsoshin na kan hanyarsu ne na bibiyar dakarun runduna na ashirin da shida (26), da aka tura aikin Operation Lafiya Dole domin fafatawa da 'yan Boko Haram.
Facebook Forum