Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Zaftarewar Laka A Habasha Ka Iya Kai 500 – Majalisar Dinkin Duniya


This grab made from a handout footage released by the Gofa Zone Government Communication Affairs Department on July 23, 2024, shows people standing at the bottom of a landslide that occurred in the Geze-Gofa district.
This grab made from a handout footage released by the Gofa Zone Government Communication Affairs Department on July 23, 2024, shows people standing at the bottom of a landslide that occurred in the Geze-Gofa district.

Iyalai da ke cikin juyayi sun cika gidaje a wani kauye da ke kudancin kasar Habasha a jiya Juma'a don yi wa ‘yan uwansu da suka mutu sakamakon mummunar zaftarewar laka da ta auku bankwana, yayin da hukumomi suka sanar da ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar.

Zabtarewar laka da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa a karamar karamar hukumar Kencho Shacha Gozdi, ta kashe akalla mutane 257, a cewar hukumar kula da ayyukan jinkai ta MDD ta OCHA ranar Juma’a, inda ta ambaci hukumomin yankin, amma ta yi gargadin cewa adadin mace-macen ka iya kai 500.

Wannan dai ita ce zaftarewar laka mafi muni da aka gani a tarihin kasar da ke nahiyar Afrika, inda masu aikin ceto ke ci gaba da neman gawarwaki.

Hukumar OCHA ta ce ta yuwu abubuwa su kara muni.

Jens Laerke, OCHA
Jens Laerke, OCHA

Kakakin hukumar Jens Laerke ya ce, "yayin da ake hasashen samun karin ruwan sama, kada a yi mamakin ganin aukuwar irin wannan bala’in a Habasha.

"A wannan yanayin, akwai bukatar mu ja hankali game da yawan tallafin da ake samu don mayar da martani, ana bukatar tallafin kasashe ga hukumomin jinkai da ke aiki a Habasha cikin gaggawa," a cewar Laerke.

'Yan kilomitoci kadan daga yankin tsaunin da ya fado kan al’umar kauyen, iyalai da ke cikin yananin bakin ciki da kidimewa sun wanke gawarwakin mutanen da aka fito da su daga cikin laka, kafin a nade su da likafani gabanin taron jana'izarsu.

"Zuciyata na cike da farin ciki saboda na gano gawar matata," abin da Ketema Kelsaye, dan shekaru 32 ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP kenan.

Zaftarewar Laka a Kencho Shacha Gozdi, kasar Habasha
Zaftarewar Laka a Kencho Shacha Gozdi, kasar Habasha

"Na yi ta kuka ina ta nemanta har tsawon kwanaki biyar, da shebur da hannawana na yi ta tona laka amma ban gan ta ba" a cewar Kelsaye. Ya kara da cewa yanzu da aka binne ta hankalinsa ya kwanta.

Majalisar dokokin kasar Habasha ta sanar da ayyana kwanaki uku don zaman makoki, da za a fara ranar Asabar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG