Gwamnatin Nigeriar dai tace ta dauki wannan mataki domin ragewa 'yan Nigeria radadin wahalar tsadar rayuwa da suke fama da ita,
Sai dai matakin yana zuwa ne adai dai lokacin da wasu kungiyoyin matasa a kasar ke shirin fita zanga zangar lumana domin nuna bacin rai akan matsananciyar tsadar rayuwa da ke ci gaba da addabar talakkawan kasar.
A hirar shi da Muryar Amurka, shugaban Hukumar kare Hakkin Dan Adam a jihar Neja kwamred Abubakar Usman yace Babu Saukin da 'yan kasa zasu samu dan araba wannan abinci.
Shi kuwa sakataren jam,iyyar SDP Mai Adawa a Jihar Kogi Hon.Dalladi Bababutum yace babu wadanda zasu ci gajiyar abincin sai wadanda ke cikin jam,iyyar APC Mai rike da Madafun iko.
A nashi bayanin, Barista Aliyu Alhasan Lauya mai zaman kansa a jihar kwara yace duk da yake yana da tabbacin wasu gwamnonin zasu kamanta wajan raba kayan abincin, sai dai i yayi kadan.
A yanzu dai 'Yan Nigeria na ci gaba da jiran isowar tirelolin kayan abincin zuwa jihohinsu domin ganin irin tasirin da zasu yi wajan rage halin matsin da 'yan kasar ke ciki.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna