Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aisha Buhari Ta Fassara Abin Da Take Nufi Da Wallafa Bidiyon Pantami


Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari (Instagram/Aisha Buhari)
Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari (Instagram/Aisha Buhari)

Karin hasken da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi na zuwa ne kasa da sa'a 24 bayan da ta wallafa bidiyon farko wanda ya janyo muhawara.

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta yi fashin baki kan wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram wanda ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

A ranar Lahadi uwargidan shugaban kasar ta wallafa bidiyon Ministan sadarwa da kula da tattalin arzikin fasahar zamani Isa Ali Pantami, inda ta saka shi yana kuka tare da mai ja masa baki a wani wa’azi da ya yi a baya kan wata aya mai da ke jan hankali kan abin da ya shafi tsoron Allah.

A karkashin bidiyo da ta wallafa na a ranar Lahadi, Aisha Muhammadu Buhari ta rubuta cewa: “Tunatarwa, a cire tsoro a yi abin da ya dace.”

Tun da ta wallafa wannan bidiyo dauke da sakon, masu fashin baki da sauran ‘yan Najeriya suke ta bayyana ra’ayoyin mabanbanta a kokarinsu na fahimtar abin da urwagindan shugaban take nufi.

Sai dai wayewar garin ranar Litinin, uwargida Aisha ta yi karin harske kan abin da take nufi da wannan sakon.

“Tafsir na Malam kan tsoron Allah ba tsoron mutum ba! Da aka cire tsoro da son kai aka shiga jihar Zamfara, abubuwa sun fara kyau. Sai a dage a shigo sauran wurare da ke bukatan haka.” Aisha Muhammadu Buhari ta ce a sakon nata na baya-bayan nan, wanda ta wallafa dauke da irin wannan bidiyon Pantami na farko.

Wasu da dama na ganin uwargidan shugaban kasar ta yi karin hasken ne, saboda ta lura ana ka-ce-na-ce dangane da abin da take nufi.

Wannan dai ba shi na karon farko da Aisha Muhammadu Buhari take fitowa tana sukar gwamnatin mijinta ba.

A wata hira da BBC, Aisha Muhammadu Buhari ta yi zargin cewa wani gungun mutane sun mamaye gwamnatinsa suna juya shi, kuma bai san da dama daga cikinsu da aka nada a matsayin jami’an gwamnatinsa ba.

Sai dai a wata hira da ya yi da VOA Hausa, Buhari ya musanta ikirarin uwargidansa, yana mai cewa, “su fadi abin da “cabal” din suka tilasta ni na yi, su fadi abu daya.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG