Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Ayi Amfani da Shafufukan Yanar Gizo ta Yadda Yakamata


Whatsapp
Whatsapp

Ana kara kira da babbar murya, akan matasa da suyi amfani da damar da suke da itana na wayar da kan matasa, ta amfani da hanyoyin yanar gizo, da majalisu da matasa kan zauna don hutawa. Wani matashi ne yayi wannan kiran.

Yace sukanyi amfani da wasu shafufukan yanar gizo don wayar da kan matasa akan hadduran dake tattare da shiga bangar siyasa. Yayi nuni da sun kirkiri shafufukan yanar gizo na facebook, tuwita, da wazob, don fadakar da matasa, kuma suna amfani da wuraren zamansu a majalisun su don fadan abubuwan da suka dace.

Yace kowane matashi yayi kokarin kare kanshi da alumarsu daga wasu haddurukan rikici a loakcin siyasa da ma sauransu. Kuma bawai sun tsaya nanka daiba. Suna kara kira ga matasa da suyi karatun ta natsu, su gujema siyar da kuri’ar su don itace yancinsu a koina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG