Jiya litinin, aka gurfanar da wani dan kasar Somalia a gaban kotun Amurka bayan da aka koro shi daga kasar Netherlands ana zarginsa da laifin bada goyon baya ga kungiyar ‘yan ta’addar Somaliya al-Shabab.
Kotun Tarayyar Amurka dake zamanta a Minneapolis, babban birnin jihar Minnesota na sauraren shari’arda ake yiwa Mahmud Sa’id Omar kan zargin baiwa wata kungiyar ta’addancin kasar waje goyon baya a shekarar 2009, kungiyar da akidar ta ita ce kisan kai, da satar mutane domin neman fansa da jikkata farra hula a kasar waje. An kuma zargi Omar da laifin raraba kudi ga matasa a birnin Minneapolis na Amurka domin suje Somalia su shiga cikin kungiyar mayakan al-Shabab.
An kuma zargi Omar da laifin zuwa Mogadishu domin rarraba kudi ga mayakan ‘yan ta’adda su sayi makamai da samun horon soja. Mahmud Sa’id Omar ya musanta wadannan zargi da ake masa.