Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Mutane 7 Sun Mutu Sanadiyar Harin Kunar Wake A Arewa Maso Yammacin Bursa A Kasar Turkiyya


Hukumomi sun ce wata mace ce ta tarwatsa kanta kusa da babban masallacin birnin,

Wani harin kunar bakin wake ya raunata akalla mutane 7 a arewa maso yammacin birnin Bursa da ke kasar Turkiyya, sannanen wurin da masu yawon bude ido ke kai ziyara.
Hukumomi sun ce wata mace ce ta tarwatsa kanta kusa da babban masallacin birnin, ita ma ta sheka lahira.
Nan take dai ba’a sami wanda ya dauki alhakin kai harin ba.
Kasar Turkiyya ta sha samun hare-hare cikin shekarar nan, ciki har da wasu guda biyu a Istanbul, birni mafi girma a kasar, wanda ‘yan kungiyar ISIS suka dauki alhaki kai shi, sannan kuma sai wasu hare-haren guda biyu da aka kai a Ankara, shi kuma ‘yan kungiyar mayakan sa-kan kurdawa ne suka dauki alhakin kai shi.
Haka kuma wata kungiya ta masu tsattsauran ra’ayin addini ita ma ta kaddamar da wasu hare-hare, yawancin akan ‘yan sanda da jami’an tsaro.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG