Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Shekaru Nawa Ya Kamata Matasa Su fara Soyayya


Kamar yadda bincike ya nuna yadda dan’adam ke canza wa daga wani lokaci zuwa wani lokaci, haka ma muhallin sa da kuma al’adun sa ke canza wa.

Idan muka dubi bangaren soyayya, al’adar soyayyar zamani da irin ta lokacin magabatan mu akwai matukar banbanci musamman ma saboda wasu dalilai na cigaba da dama da dan adam ya samu a rayuwar sa.

Abin tambaya anan shine, a mizanin shekaru nawa ya kamata iyaye su bar ‘ya’yan su, su fara soyayya?. Haka kuma matasan da kansu, wane lokaci ne a irin nasu tunanin ya kamata su fara soyayya?.

Yawancin samari da 'yan matan da dandalin VOA ya tattauna da su, sun bayyana cewar a ra'ayin su ya kamata matashi ko matashiya su kai akalla shekaru ashirin da wani abu da haihuwa kafin su fara tunanin fara soyayya.

Wasu daga ciki kuma sun nuna cewar shekaru goma sha shidda ne daidai domin ko aganin su lokacin mutum ya kamata ya fara mallakar hankalin kansa daga wannan lokaci.

Menene ra'ayin ka dangane da wannan bayani? kana dan shekaru nawa ka fara soyayya kuma wanne irin kalubale ka fuskanta?

Ku bayyana mana ra’ayin ku a shafin mu na facebook.com/dandalinvoa

XS
SM
MD
LG