A hirarshi da aka yi da shi ne, Mahmoud Dicko yake gayawa Sashen Faransanchi na gidan rediyon nan na Muryar Amurka, cewa lalle ya nemi sulhu da kungiyar ta Ansar Dine, kuma madugunta Iyad ag-Ghali ya amsa cewa sun karbi sulhun.
Sai dai kuma a amsar da ya bada, Ghali yace ba zasuyi aiki da “duk wanda bai yarda da Shari’a ba”, abinda yasa ake zaton ko wannan wani sharadi ne yake gittawa.
Ita kungiyar Ansar Dine tana daya daga cikin kungiyoyin Islama guda ukku da suka kama yankin arewancin Mali a shekarar 2012.
Daga baya ne sojan Faransa suka fitar da su daga yankin, amma tun lokacin mayakan kungiyar ke ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar ta Mali.