Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin Kan Koutoukale A Nijar


Barnar da aka yi a gidan kason Koutoukale
Barnar da aka yi a gidan kason Koutoukale

Kungiyar ISIS ta sanar da duniya a sashenta na Al-Akbar a yanar gizo dake da ofishi a kasar Mauritania cewa ita ce take da alhakin kai hari a gidan kason Koutoukale.

Harin an kai shi ne ranar Litinin 17 ga watan nan na Oktoba wanda ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin maharan tare da kona baburan dake wajen gidan kason.

Sanadiyar harin ne ya sa wasu 'yan kasar Nijar suka gargadi gwamnati ta dauki matakan shigar da jama'ar kasar a harkokin tsaro. A cewar shugaban kungiyar muryar talaka Hassan Nasiru Seidu hakan zai taimakawa jami'an tsaro su samu bayanan siri a lokacin da ya dace.

Malam Seidu yace kungiyoyi irin su ISIS kungiyoyi ne dake da mabiya a cikin gidajen mutane a kasashe daban daban na duniya. Dole ne a ja hankalin gwamnati ta karfafa kokari bisa ga binciken harin Koutoukale. Yace hankalin jami'an tsaron kasar har yanzu da tunanensu kamar irin na da ne, wato na lokacin mulkin mallaka. Basu shaku da talaka ba balantana talaka ya yadda ya basu labarin da yakamata. Baicin hakan, a cewar Seidu idan an basu labarin ma yana ya zama wa mutum wata matsala. Suna iya juyawa su tilasta ma mutum ya bayyana idan ya samo labarin ko kuma a tafi da mutum inda baya zato.

Malam Seidu yace yakamata jami'an tsaro su kwantarwa talakawa hankali, su yadda dasu domin su dinga kawo masu labari ingantacce dare da rana.

Mutuwar sojoji 22 a rana tsaka a sansanin 'yan gudun hijira daga Mali dake jihar Tawa wani abu ne da 'yan Nijar ke kwatantawa da sakacin jami'an tsaro kamar yadda hukumomin kasar suka ce sun gano wani abun da yayi kama da harsashen jama'a.

Talilin haka Nasiru Seidu yace akwai abubun da jama'a basu iya ganewa kamar yadda wasu jami'an tsaro ke cewa basu da kayan aiki. Yakamata a ce kullum jami'an tsaro suna cikin shirin ko ta kwana.

Tabarbarewar zamantakewa tsakanin jami'an tsaro da talakawa na cikin matsalolin da suka addabi kasar a yau, inji Dr Sani Yahaya Jinjina wani masanin tsarin zamantakewar dan Adam wanda yake ganin lokacin hadin kai yayi. Kutuntawar da sojoji ke yiwa jama'a ya sa suka fita daga harkokinsu. Ya kamata su dinke wannan barakar domin idan ba talaka ya bada goyon baya ba duk wani abun da sojoji suka shirya da ya jibanci tsaro ba zai yi tasiri ba. Ya bada shawarar a kafa kwamitocin tsaro na farar hula a unguwanni daban daban domin inganta tsaro.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye


q

XS
SM
MD
LG