Fazulla Wahidi, wanda tsohon gwamnan Lardin Herat ne, ya gayawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an ceci shi ne a wajen wani shingen binciken ‘yan sanda da ke arewa maso yammacin Pakistan a birnin Peshawar.
Ya kara da cewa an yi ta musayar harbe-harbe bayan da aka ceto shi, kuma ya kara da cewa bai san wadanda suka yi garkuwan da shi a Islamabad ba makwanni biyu da suka gabata.
‘Yan sandan Pakistan sun gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa suna tsare da wasu mutane uku da ake zargi na da hanu a garkuwar da aka yi da tsohon gwamnan Lardin na Herat.