Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Barkewar Cutar Gubar Dalma a Jihar Zamfara


Sama da yara 100 ne aka ruwaito sun kamu da cutar, sannan an kwantar da su a asibitoci daban - daban a jihar.

Cutar da ta bayyana ta fi tasiri akan yara kanana. Daga cikin alamomin cutar, tana kumbura wa yara ciki Sosai. mai kula da al'amuran Lafiya a matakin farko a karamar hukumar Bungudu, Bashiru Muhammad Bungudu ya ce, lamarin yayi Kamari a kauyuka da dama, kuma ta na bayyana ne a jikin kananan yaran.

wakilin Muryar Amurka a Zamfara Abdulrazak Bello Kaura ya ruwaito cewa Bashir ya ce “Yara ‘Yan shekara biyar zuwa sha biyu suna kamuwa da cutar, cikin su yana kumbura kamar Kwarya, suna fama da zazzabi da kasala da kuma Amai."

Dr. Nafisa Muhammed Maradun Kwamishiniyar Lafiya ta jihar Zamfara, ta bada tabbacin bullar cutar, inda ta ce ya zuwa yanzu kimanin kananan yara 102 ne suka kamu da cutar kuma hudu daga cikin su sun riga mu gidan gaskiya.

A zantawar da Abdulrazak yayi da Dr.Nafisa Maradun, ta ce “Daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta dauka, akwai tura kwararru don gano nau’in cutar da kuma bude cibiyar kula da marasa lafiya inda za mai da hankali akan kula da cututtuka na musamman da kuma Matakan hana yaduwar cutar.”

Ta kara da cewa, lamarin yafi muni a kananan hukumomi, wadanda suka hada da Maradun, Bakura, Talata Mafara, Gummi, Bukkuyum, Maru, Bungudu da kuma Tsafe duka a cikin jihar Zamfara.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG