Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Taba Juyawa APC Baya Ba - Buhari


Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Kalaman na Buhari na zuwa ne sa’o’i bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya ce ya fadawa Buhari cewa zai fita a jam’iyyar ta APC kamaryadda rahotanni suka nuna.

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce jaddada matsayarsa ta ci gaba da zama matsayin mamba a jam’iyyar APC mai mulki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ta hannun kakakinsa Malam Garba Shehu, Buhari ya ce shi da APC – mutu ka raba.

“Ni mamba ne a APC kuma ina so a rika kirana a matsayin hakan. Zan yi iya bakin kokarina na ga na tallata APC ta kowacce hanya.” Buhari ya ce cikin sanarwar.

Kalaman na Buhari na zuwa ne sa’o’i bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya ce ya fadawa Buhari cewa zai fita a jam’iyyar ta APC.

A farkon makon nan El Rufa’i ya sauya sheka ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) mai alamar doki yana mai zargin jam’iyyar da kaucewa manufofin da aka kafata akai.

Sai daia sanarwar ta Garba Shehu, Buhari ya ce, “ba zai taba juyawa jam’iyyar baya ba wacce ta bas hi wa’adin mulki biyu a ofis.”


Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG